Da Pence da Kaine sun fafata ne a muhawararsu daya tilo kafin zaben da za a gudanar a watan gobe, inda su ka yi ta katse ma juna hanzari yayin da su ke muhawara kan makaman nukiliya, da halin da ake ciki a Siriya da kuma batun bukatar sauyi a dokar manyan laifuka na cikin gida.
Pence ya bayyana Hillary Clinton da "kanwa uwar gabi" game da manufofin Shugaba Barack Obama na kasashen waje, wadanda ya ce sun jefa Gabas Ta Tsakiya "cikin radami." Ya zargi Hillary Clinton da sakacin da ya yi sanadin bullar ISIS, da kuma abin da ya kira, "sabuwar Rasha mai gaba-gadi."
Shi kuwa Kaine cewa ya yi, Trump mutum ne mai fifita kansa, sannan ya zargi Trump da yin huldar cinakayya da Rasha, wadanda ya ki ya bayyana.
To amma 'yan takarar biyu sun yi muwafaka kan bukatar yin wani abu na kare farar hula a arewacin Siriya. Pence ya ce ya kamata matakan da za a dauka su hada da hana jiragen yaki kutsawa cikin wani yankin na sararin sama, kuma muddun Rasha ta cigaba da kai hare-hare kan birnin Aleppo, to sojojin Amurka su shiga kai hare-hare kan muradun sojin Siriya a matsayin martani.
Hakazalika, bakinsu ya zo daya kan bukatar kafa hukumar sa ido ta al'umma, amma ba su cimma jituwa kan sauran batutuwan sauye-sauye a fannin shari'ar manyan laifuka ba.
Pence ya ba da shawarar a yi amfani da tsarin nan na tsayarwa da kuma binciken duk wanda ake shakkarsa, sannan ya ce kar Amurkawa su rinka yin mummunan zato ga 'yansanda idan wani dan sanda ya kashe wani mutum, a yayin da shi kuma Pence ya yaba da shawarar Clinton kan dakile wanzuwar bindiga da kuma kula da masu tabuwar hankali.
Kaine ya kuma bukaci Trump ya bayyana takardar shaidar biyan harajinsa, wadda 'yan Democrat da dama su ka yi imanin cewa za ta nuna cewa ko da ma ya biya haraji ga gwamnatin tarayya abin da ya biya cikin shekaru da dama bai da yawa. Pence ya kare attajirin jagabansa da cewa dan kasuwa ne mai kwazo, wanda ya kirkiro ayyukan yi wa dubban mutane.