'Yan arewan da suka halarci taron sun nuna takaicinsu akan yadda ake yawan samun tashe tashen hankula a yankin fiye da kima tare da koma bayan tattalin arziki da rashin ba matasan yankin jagoranci ingattace.
Sagiru Hamidu ya ce ra'ayinsa tamkar abubuwan da suka damu mahalarta taron ke nan. A cewarsa alamuran arewa sun tabarbare. Ya ce babu kasuwanci, babu gonaki , babu tsaro babu ilimi. Matasan arewa sun kusa zama dukansu 'yan kwaya ne, injishi. Rashin abun yi ya sa matan arewa sun zama sake. Dole ne a tashi tsaye yanzu a fuskanci matsalolin.
Hajiya Mero Habib ta koka akan yadda manyan arewa suka dade suna mulki amma yankin bai canza ba. Ta ce sukan fadi abubuwan da Sardauna ya yi amma su sun ki yin komi sun gwammace su azurtar da 'yan matansu. Tana fatan taron zai kawo gyara.
Amma sakataren kungiyar Dr. Umar Ardo ya ce lokaci ya yi a tashi a gyara illolin da suka addabi yankin. Ya ce bai kamata arewa ta zauna haka ana zaginta ba kan cewa bata iya ba..
Kungiyar dai ta kafa kwamitoci biyar da zasu yi aiki tukuru domin cimma burinsu..
Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani.
Facebook Forum