Ziyarar wasu kasashen Afirka da sakataren harkokin Amurka Rex Tillerson ya fara ranar shida ga wannan watan ta haddasa ra'ayoyi masu karo da juna tsakanin 'yan Najeriya.
Ziyarar ita ce ta farko da wani babban jami'in gwamnatin Amurka zai kai nahiyar Afirka tun lokacin da Shugaban Amurka Donald Trump ya karbi madafin ikon kasar.
Ra'ayin 'yan Najeriya sun banbanta akan mahimmanci ko rashin mahimmancin ziyarar ta Mr. Rex Tillerson. Wasu na ganin shugaban Amurka na yanzu ba mutumin da ya kan so ya ba kasashen waje tallafi ba ne musamman kasashen Afirka. Baicin haka mutum ne dake da saurin canza ra'ayinsa ko manufofin kasar.
Ambassador Lawal Munir wani tsohon jakadan Najeriya ya yi tsokaci akan ziyarar ta Mr. Tillerson. A cewarsa Shugaba Trump tun lokacin da ya kama mulki ya nuna kasashen Afirka basu isa a dama dasu ba, har ma ya ce duk taimakon da kasarsa ke ba Afirka zai dakatar. Abu dake biye da wannan shi ne yadda Shugaba Trump ka iya canza komi bisa ga irin maganganunsa. Injishi ba mutum ba ne da za'a iya rike maganarsa a kuma dogara a kanta.
Amma ra'ayin Ambassador Jibrin Cinede ya banbanta. Shi ya ga mahimmancin ziyarar. Injishi Rex Tillerson zai san abun da ya damu kasar ya bayyanawa Shugaba Trump. Akan cewa Trump na iya birkitar da komi, Ambassador Jibrin ya ce dole ne ya saurari Tillerson domin ya san wasu abubuwa game da Afirka. Ya ce saduwa da manyan kasashen duniya ba lallai sai sun ba da taimako ba. Akwai wasu abubuwa kamar kasuwanci, arzikin kasa da karatu da kiwon lafiya tare da sanin juna da zasu zama da anfani.
Ga rahoton Umar Faruk Musa da karin bayani.
Facebook Forum