Gwamnatin Najeriya na kara kare manufarta ta hana shigo da shinkafa daga kasashen waje ta kan iyakokinta.
Hakan ya kai ga noma shinkafar cikin kasar tare da gina kamfanonin sarrafa ta. Ministan Noma na Najeriya, Audu Ogbeh, ya ce jakadan Thailand a Najeriya ya shaida masa cewa kamfanoni bakwai na kasar sun durkushe sanadiyyar kin sayen shikafarsu da Najeriya ta yi.
Manoman shinkafa a Najeriya na bunkasa sakamakon hana shigo da ta kasar Thailand. Gwamnan Kebbi Atiku Bagudu, jihar da yanzu ta yi fice wajen shukawa da sarrafa shinkafa, ya ce su kam sai hamdala. In ji shi niyyar ciyar da kasar da shinkafa ta tabbata domin ana nomanta koina. Jihar Kebbi ta kara yawan shinkafar da take nomawa.
Sanadiyar bunkasa ayyukan noma ya sa Najeriya na ci gaba da bude tasoshin jiragen ruwa na tudu a arewacin Najeriya da bashi da gabar teku domin manoma su samu damar fitar da albarkatun gonakansu zuwa kasashen waje..
Hassan Bello shugaban hukumar tashar jiragen ruwa ya ce baicin fitar da kayan gona waje kowace tasha ka iya daukan ma'aikata daga dubu biyar zuwa takwas. Masana'antoci zasu taso. Haka otel otel da hanyoyi da za'a gina. Ko mutanen Nijar zasu kawo kayansu tasoshin domin kaisu teku su fita zuwa kasashen waje. Akwai tasoshin da yawa amma na Jos da Funtua su e suka fi kan gaba.
Jagoran bude tashar Funtua Umar Muttalab ya ce nan da watan biyar zasu fara aiki a tashar ta Funtua. Kasashe irin su Nijar da Burkina Faso da ire irensu zasu anfana da tashar.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.
Facebook Forum