Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda Sun Gano Mutumin Da Ya Kashe Wasu Mata A Florida


'Yan sanda a Yoga Studio a Florida
'Yan sanda a Yoga Studio a Florida

‘Yan sanda a jiya Asabar sun gano mutumin nan da ya kashe wasu mata biyu a wani wurin motsa jiki wato Yoga studio dake Tallahassee na jihar Florida kafin ya kashe kansa.

‘Yan sandan sun ce sunan maharin Scott Beierle dan shekaru 40 da haifuwa mazaunin Deltona a Florida. An kuma gano mata biyun da aka harbe a shekaranjiya Juma’a da sunaye Maura Binkey mai shekaru 21 kuma daliba a jami’ar jihar Florida da kuma Nancy Van Vessem mai shekaru 61 a duniya da suke tare a jami’ar.

Wasu mutane biyar kuma sun ji rauni yayin da Beierle dan shekaru 40 ya shiga wurin motsa jiki mai cike da jama’a da yammacin ranar Juma’a ya fara harbi. ‘Yan sanda sun ce mutanen da suke cikin wurin sun yi rigima da Beierle domin kare kansu.

Bayanan ‘yan sanda ya nuna Beierle tsohon dalibi a jami’ar Florida FSU a takaice wanda ya taba aikin soja, an kama shi sau biyu a jami’ar a kan laifin rigima da mata. An kuma gano ya dora bidiyo a shafin YouTube yana bababtu a kan kalaman wariyar jinsi wurin huldar mace da namiji da kuma mata da suka ki yarda su yi hulda da shi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG