Shugaban kasar Lebanon ya nada Najib Mikati da kungiyar Hezbollah ke marawa baya a matsayin Firai Minista yayinda ake ci gaba da zanga zanga a kasar yau Talata a birane da dama, na nuna adawa da karin tasirin siyasar da kungiyar mayaka ta ‘yan Shi’a a Lebanon ke samu. Ofishin Shugaban kasa Michel Suleiman ya bada sanarwar wannan zabin da zai ba Mr. Mikati ikon jagorancin rawar kafa sabuwar gwamnati. ‘yan majalisar dokokin kasar Lebanon sun goyi bayan zaben Mr. Mikati inda ‘yan majalisa sittin da takwas daga cikin daru da ishirin da biyu suka nuna goyon bayan zabenshi ya maye gurbin PM Saad Hariri wanda ya sami kuri’u sittin. Mr. Mikati ya taba rike mukamin Firai Minista cikin shekara ta dubu biyu da biyar. A halin da ake ciki kuma, zanga zangar da kungiyar Hezbolla ta ‘yan Sunni take yi, ta rikide ta zama tashin hankali. Dubban magoya bayan Hariri sun taru a Tripoli domin abinda suka kira ranar zanga zangar nuna fushi.
Shugaban kasar Lebanon ya zabi Najib Mikati da kungiyar Hezbollah ke marawa baya a matsayin sabon firai minista
Labarai masu alaka
Nuwamba 09, 2024