‘Yan sanda a Kwango-ta-Kinshasa sun bayyana kimanin mutanen dari a bainin jama’a wadanda aka kama dangane da harin da aka kai makon jiya a kan gidan shugaba Joseph Kabila a birnin Kinshasa. Wadansu daga cikin wadanda aka kama sun nuna alamun raunata yayinda suka wuce manema labarai suna dingishi jiya Litinin. Wadansu sun rika cewa, basu da hannu a kai harin. Jami’an kasar Congo sun ce an kama mutane dari da ishirin da shida sabili da rawar da suka taka a harin da aka kai ranar ashirin da bakwai ga watan Fabrairu a gidan shugaban kasar. An kashe mutane goma sha tara da suka hada da sojoji takwas, lokacin da mutane dauke da bindigogi da adduna suka kai farmaki kan gidan. Dogarawan dake tsaron lafiyar shugaban sun samu nasarar fatattakarsu. Babu wanda ya dauki alhakin kai harin kuma ba a san musabbabin kai shi ba. Mr. Kabila ya hau karagar mulki a Kwango-ta-Kinshasa ne bayan da aka yiwa mahaifinsa, Laurent Kabila kisan gilla a shekara ta dubu biyu da daya. Mr. Kabila ya lashe zaben damokaradiya na farko da aka gudanar a Congo cikin shekara ta dubu biyu da biyu zai kuma sake tsayawa takara bana.
Yan sanda sun bayyana mutanen da ake kyautata zaton suna da hannu a kai harin gidan shugaban Congo ta Kinshasa
'Yan sanda a Kwango-ta-Kinshasa sun bayyana kimanin mutanen dari a bainin jama’a wadanda aka kama dangane da harin da aka kai makon jiya a kan gidan shugaba Joseph Kabila