‘Yan Nijeriya na shirin zaben shugaban kasa, a daidai lokacin da wannan kasar da ta fi yawan jama’a a Afirka ke kokarin kawo karshen tarihinta na gudanar da zabe mara inganci.
Wasu na ganin shugaba Goodluck Jonatahn na jam’iyyar PDP mai mulki na iya cin zaben. To saidai fa manyan abokan karawarsa na kokarin kulla kawancen da ka iya sawa a je ga zagaye na biyu na zaben fidda gwani.
Jami’an manyan jam’iyyun adawan sun ce an tattauna tsakanin ‘yan takararsu, wato Muhammadu Buhari da Nuhu Ribadu.
Buhari, na da mutukar magoya baya a arewacin kasar. A sai’ilinda shi kuma Mr. Jonathan ke da dinbin goyon baya a kudancin kasar.
A halin da ake ciki dai sakamakon zaben majalisar dokokin kasar na ran Asabar ya nuna cewa jam’iyyar PDP mai mulki ta yi rashi sosai, to amman har yanzu it ace za ta yi rinjaye a Majalisar.
Bayan zaben ‘yan Majalisar Dokoki a watan jiya, ‘yan Nijeriya za su sake kada kuri’a a wannan Asabar din. Mariama Diallo ta tubi abin da ya fi muhimmanci a wannan marrar, a daidai lokacin da mutanen wannan kasar da ta fi yawan mutane a Afirka ke shirin zaben shugabansu na biye.
A wurin wani kamfe a Lagos, babbar cibiyar kasuwancin Nijeriya Muhammadu Buhari, shugaban daya daga cikin jum’iyyun adawa, mai suna CPC, ya gaya wa taron jama’a cewa duk da dinbin arzikin man Nijeriya, har yanzu ‘yan kasar ba su ga wani alfanu abu.
Muhammadu Buhari y ace, “Ina kudin? Me ya sa abubuwa su ka lalace? Cin hanci da rashawa, wannan shi ke zagon kasa ma Nijeriya.”
Buhari ya fara shugabancin Nijeriya ne a 1983 kuma wasu daga cikin masu goyon bayansa sun ce har yanzu sun a tune da yakin day a yi da cin hanci da rashawa. To amman ya yi shekaru biyu ne kawai bisa gadon mulki saboda sojoji sun hambare shi.
A nashi yakin neman zaben kuma, shugaba Goodluck Jonathan ya yi alkawarin inganta bangaren kiwon lafiya, da ilimi da kuma tattalin arziki.
Shugaba Goodluck Jonathan y ace, “Ida nana son a ciyar da kasa gaba daga matsayin kasa mai tasowa zuwa kasar da ta ci gaba kamar yadda aka yi a wasu wuraren, dole a maid a hankali kan tattalin arziki. Shi ne ya fi muhimmanci.”