Yayin da ‘yan Najeriya ke shirin fara kada kuri’u a zaben ‘yan majalisar dokokin tarayya yau asabar a fadin kasar, fashewar bam a wani ofishin hukumar zabe da kuma harin da aka kai kan wani wurin tara kayayyakin zabe sun hallaka mutane akalla 12.
Wadannan hare-hare a Suleja, dake bayangarin Abuja, babban birnin kasar, da kuma Jihar Borno a arewa maso gabashin kasar, sun abku da maraicen jiya jumma’a.
‘Yan sanda sun ce mutane 8 suka rasa rayukansu a fashewar bam a ofishin hukumar zabe a Suleja. Suka ce wannan fashewar ta kuma raunata mutane da dama.
A Jihar Borno, ‘yan sanda suka ce wasu ‘yan bindiga sun harbe suka kashe mutane 4 a lokacin da suke shirin rarraba kayayyakin zabe. ‘Yan sanda suka ce daya daga cikin mutanen da aka kashe jami’i ne na jam’iyyar PDP.
Najeriya tana kara tsaurara matakan tsaro domin zaben na yau asabar, inda a jiya jumma’a ma’aikatar harkokin cikin gida ta Najeriya ta rufe dukkan bakin iyakokin kasar, su kuma ‘yan sanda suka kara yawan sintiri tare da takaita zirga-zirgar ababen hawa a kan tituna. Har ila yau, sojoji su na sanya idanu a kan rumfunan zabe.
A ranar alhamis da daddare, ‘yan sanda a Kaduna dake arewacin Najeriya, sun ce wani mutum ya sheka barzahu a lokacin da wani bam da yake kokarin hadawa ya tashi haka kwatsam.
A bayan zaben na yau, Najeriya zata gudanar da zaben shugaban kasa ranar asabar 16 ga wata, sai kuma zabubbuka na jihohi a ranar 26 ga wata.
Babban jami’in diflomasiyyar Amurka mai kula da harkokin nahiyar Afirka, Johnnie Carson, yana daga cikin wadanda zasu kalli yadda za a gudanar da wannan zabe na Najeriya. Carson yayi gargadin cewa ‘Yan Najeriya zasu komo daga rakiyar shugabanninsu da kuma yunkurin shimfida dimokuradiyya a kasar idan har wadannan zabubbuka na bana ba su fi zabubbukan da aka yi a 2007 ba. An fuskanci tashe-tashen hankula da mummunan magudi da kuma rudu a zabubbukan na 2007, abinda har ya sa KTT ta bayyana wadancan zabubbuka a zaman marasa halalci.