A jawabin da shugaban jam’iyyar ACN ya yiwa taron manema labarai a shalkwatar jam’iyyar CAN ta kasa a birnin Abuja, shugaban jam’iyyar na kasa kuma tsohon Gwamnan jihar Osun dake Kudu Maso yammacin Nigeria, Chief Bisi Akande, bai bada wani kwakkwaran dalilin da tattaunawar hadin kan jam’iyyu biyu ya wargaje ba tare da an kai ga cimma daidaituwar tsaida dan takarar shugaban kasa guda ba.Amma ya furta cewar bayan an kammala zaben shugaban kasa a ranar Asabar ba’a sami fidda dan takarar day a sami Nasara a lokaci guda ba, lokacin ne jam’iyyar CAN zata san irin matakin da zata dauka. Amma shugaban na jam’iyyar CAN ya kumayi zargin rashin samun cikakken hadin kai daga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar CPC kuma tsohon shugaban Nigeria Janar Muhammadu Buhari.
A halin da ake ciki, ‘yan Nigeria sun fara bayyana ra’ayinsu game da rashin samun nasarar yarjejjeniyar tsaida dan takarar guda daga jam’iyyun CAN da CPC, a rahoton da wakilin mu a birnin Ibadan yammacin Nigeria Hasan Umaru Tambuwal ya aiko mana, mafi yawan al’ummar Yammacin Nigeria, Yarabawa da hausa sun nuna takaicin hakan.