Kididdigar rabin yawan kuri’un da jam’iyyu suka samu ta nuna jam’iyyar hamayya ta (ACN) tayi ba zata a samun yawan kujeru a yankin Kudu Maso Yammacin Nigeria. Kazalika ita ma jam’iyyar (CPC) tayi rawan gania jihohin Arewa. Jam’iyyar CPC Karkashin inuwarta ce tsohon shugaban Gwamnatin mulkin sojin Nigeria Muhammadu Buhari zai yi takarar shugaban kasa, ana kuma kyautata cewar shine a sahun gaban masu tinkarar shugaba mai ci Goodluck Jonathan a zaben Asabar mai zuwa.
Jami’an kallo na kungiyar Tarayyar Turai, ran litinin suka bada sanarwar cewa zaben Asabar da ta gabata anyi shi cikin yanayin zaman lafiya da kwanciyar hankali, hakan kuma yana karfafa gwiwar kasa da kasa An sami nasarar gudanar dazaben duk da barazanar tada bom da aka yi a Suleja da Maiduri. An dage gudanar da zaben har sau biyu saboda rashin isar kayan aiki wuraren zaben dake gunduma da majalisun kananan hukumomin Nigeria.