Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan Najeriya Za Su Fara Biyan Harajin ₦200 A ATM


Wani yana rike da Naira
Wani yana rike da Naira

Karin cajin cirar kudi na ATM da Gwamnatin tarayya ta aiwatar, wanda a baya yake a matsayin ₦35, yanzu zai koma ₦200 har zuwa ₦500, ya jawo ce-ce-ku-ce tsakanin ƴan kasar

‘Ƴan kasar dai na ci gaba da kokawa bisa yadda Gwamnati ke ci gaba da kakaba musu sabbin haraji.

Masana tattalin arziki dai na ganin hakan wata barazana ce ga talakawan kasar da kudin shigar su bai taka kara-ya-karya ba, kuma hakan zai sa ƴan kasar su kauracewa ajiye kudaden su a bankuna.

A wata sanarwar da sashin sadarwar na babban bankin Najeriya CBN ya fitar, babban bankin ya umurci dukkanin bankuna da cibiyoyin kudi na kasar da su aiwatar da sabon tsarin cajin kudi na ₦200 a duk adadin kudin da ya kai ₦20,000 da aka cire a na’urorin cirar kudi na bankuna (ATM) kuma umarnin zai fara aiki ne ranar 1 ga Maris din shekarar da muke ciki.

A cewar babban bankin, sabon tsarin cajin kudin na ATM ya zama musu tilas ne, idan aka yi la’akari da yadda hauhawar farashin gudanar da ayyuka da kuma hada-hadar kudade ya karu a kasar, sai kuma bukatar kara inganta yadda ayyukan na ATM suke.

Sanarwar ta kara da cewa, tsarin cajar kudin na ATM din, zai shafi wanda suka yi huldar cirar kudin a ATM din bankunan da basa hada-hadar kudade tsakanin su, sai dai bankin ya kara da cewa, ba za a caji koda sisin kobo ba, ga wadanda suka yi huldar cirar kudi a bankunan da suke hada-hada.

Ƴan kasar dai na bayyana rashin jin dadin su game da wannan sabon tsari.

Dr. Isa Abdullahi Kashere dake nazartar harkar tattalin arziki a jami’ar tarayya ta Kashere a Jihar Gombe, na ganin wannan sabon tsarin haraji ka iya kawo wa tattalin arzikin kasar nakasa.

Yanzu abin jira a gani shi ne yadda gwamnatin kasar za ta aiwatar da sabbin ayyukan ci gaba a kasar, bayan kare-karen haraji da ta bijiro da su.

Saurari cikakken rahoto daga Rukaiya Basha:

‘Yan Najeriya Za Su Fara Biyan Harajin ₦200 A ATM.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG