Gwamnatin Najeriya ta bukaci babbar kotun tarayya dake Abuja ta tilastawa kamfanin musayar kudaden kirifto, Binance Holdings Nigeria, ya biyata dala biliyan 79.51 da Naira miliyan 231 saboda zargin cewa ayyukansa a kasar sun janyo mata asarar tattalin arziki.
A yau Laraba, Hukumar tara haraji ta tarayyar Najeriya (FIRS), ta bukaci Binance ya biyata dala biliyan 2.001 na harajin kudaden shigarsa na shekarun 2022 da 2023.
A kunshin karar, ana zargin Binance da 2 daga cikin manyan jami’ansa, Tigran Gambaryan da Nadeem Anjarwalla da karya dokokin Najeriya, ciki har da kin yin rijista da FIRS domin biyan haraji abinda ya sabbabwa Najeriya asarar tattalin arziki a wannan dan tsakani.
Karar ita ce ta 3 dake gaban kotu akan kamfanin Binance a halin yanzu.
Dandalin Mu Tattauna