Amurka ta ce za ta bayar da tallafin dala miliyan dari biyar da talatin da uku (533 miliyan) ga kasashen Afirka kamar Najeriya, da Habasha, da Somaliya, da Sudan Ta Kudu da kuma kasashen da ke yankin Tabkin Chadi, wato kasashen da ke fama da karancin abinci sakamakon rikici ko suka yi fama da fari na tsawon lokaci.
Sakataren Harkokin wajen Amurka, Rex Tillerson ne ya yi wannan sanarwar yau a Jihar Virginia gabanin ziyarar da zai kai wasu kasashen Afirka guda biyar, ciki har da Najeriya.
Wannan karin kudaden tallafin daga Amurka zai taimaka wajen samar da agajin abinci ga masu bukata, da samar da tsaftataccen ruwan sha, da agajin gaggawa na kiwon lafiya musamman ta wajen dakile cututtuka masu yaduwa a cikin al’umma da sauransu.
A cewar ma’aikatar harkokin wajen Amurka, wadannan kudaden tallafin za a rarraba su kamar haka: Sudan ta kudu za ta samu kusan dala miliyan 184, Habasha da Somaliya kowanensu zai samu sama da dala miliyan 110, sannan kuma dala miliyan 128 zai je ga Najeriya da sauran kasashen da ke yankin tafkin Chadi.
Amurka ta kasance kasar da fi kowacce bayar da taimakon agaji ga kasashen Afirka masu fama da rikici, inda tun daga farkon shekarar 2017 ta bayar da kusan dala biliyan uku.
Facebook Forum