Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Najeriya Miliyan 18 Ke Fama Da Cutar Cancer - WHO


Tambarin Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO
Tambarin Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO

Hukumar lafiya ta Duniya WHO, ta ce Najeriya ce kasar da aka fi samun mace-macen masu fama da cutar cancer ko daji a nahiyar Afirka.

A cewar hukumar, rashin fadakarwa, da gano cutar a kurarren lokaci, da tsadar magungunan cutar, na daga cikin manyan dalilan da ke sa ake samun yawaitar mace-macen masu dauke da cutar ta cancer a Najeriyar, wacce ke yammacin nahiyar ta Afirka.

Wani Kwararren likita a Najeriya, Aminu Aliyu ya ce “a tsakanin shekarar 2012, an samu karuwar mutanen da ke kamuwa da cutar daga adadin miliyan 12 zuwa 14 har zuwa miliyan 18 a bara."

Ya kara da cewa, ya zuwa yanzu, ba a fitar da alkaluman wannan shekara ba.

A irin matakan da take dauka, gwamnatin Najeriya, ta kaddamar da wasu tsare-tsare na yaki da cutar, inda ko a farkon makon nan, ta ayyana zaftare kudaden da masu dauke da cutar za su kashe, wajen yin magani da kashi 50 cikin 100.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG