Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kafa Rundunar Kare Dazuka A Nasarawa


Mataimakin gwamnan jahar Nasarawa, Dakta Emmanuel Akabe, da Mai Martaba Sarkin Lafiya Sidi Bage Muhammad da shugabannin dogarawan tsaron dazuka
Mataimakin gwamnan jahar Nasarawa, Dakta Emmanuel Akabe, da Mai Martaba Sarkin Lafiya Sidi Bage Muhammad da shugabannin dogarawan tsaron dazuka

Ganin yadda aka kafa wannan runduna ta dogarawan tsaron dazuka a jahar Nasarawa a daidai lokacin da miyagu ke dada yawa da daji, ba shakka za a yi maraba lale da wannan rundunar - musamman ma idan su ka ga rundunar ta firgita miyagun cikin dajin.

Mai Martaba Sarkin Lafiya kuma shugaban majalisar sarakunan jahar Nasarawa, Mai Shari’a, Sidi Bage Muhammad ya ce dawo da tsarin bai wa sarakuna hurumin kula da dazuka, zai taimaka wajen ganowa da hana batagari buya a daji suna aikata ta’asa kamar garkuwa da mutane da fashi da makami da dai sauransu.

Basaraken ya bayyana hakan ne yayin da hukumar tsaro da ba da kariya wa al’umma ta kasa a jahar Nasarawa ta kaddamar da wata hukuma da za ta kula da dazukan jahar.

Sarkin na lafiya ya ce hukumar za ta kuma taimaka wajen sasanta tsakanin manoma da makiyaya.

Mataimakin gwamnan jahar Nasarawa, Dakta Emmanuel Akabe ya ce gwamnati za ta ci gaba da mara wa hukumar baya don samar da tsaro a jahar.

Kwamandan hukumar Civil Dafence a jahar Nasarawa, Muhammad Gidado Fari ya ce jami’an sun sami horo na musamman ta yadda za su tinkari ‘yan ta’adda.

Ga wakiliyarmu Zainab Babaji da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:22 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG