Kungiyar tana son tantance irin gudummawar da zata bayar domin inganta zabukan kansiloli da na majalisun karkara da za'a yi a farkon shekarar dubu biyu da goma sha bakwai sun gudana cikin kyakyawan yanayi.
'Yan ba ruwanmu sun ce tawagar tana kasar ne ta duba zaben da aka yi can baya a kasar. Suna san su lalubo bakin zaren yadda za'a gyara kuskuren da aka yi a zabukan baya. Manufar ita ce a tabbatar cewa zabukan gaba sun fi na da kyau.
Mahalarta taron, wasun su sun ce zabukan na baya suna kawai suka tara amma ba inganci ba saboda haka a bar kaza cikin gashinta. Kokari za'a yi a gyara saboda gobe. A gyara kada Nijar ta lalace.
Kungiyar ta sanar cewa zata shirya wani taron karawa juna sani ta hada duka bangarorin siyasa da na fararen hular Nijar a nan gaba kadan domin fadakar dasu akan wasu mahimman dabaru da zasu taimaka wajen kaucewa kurakuran da zasu lalata zabe.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.