Kusan ‘yan majalisu 40 daga cikin 73, na neman Kakakin Majalisar, Alex Tyler, ya sauka daga mukaminsa, yayin da ya ke fuskantar tuhuma kan zargin karbar cin hanci.
Wani mai taimakawa alkali a sauraren shari’a, ya zargi Tyler da wasu jami’an gwamnati da wani dan kasuwar da wani kamfanin kasar waje mai hakar ma’adinai, da hanu a wannan badakala, kamar yadda wani rahoton kungiyar nan da ake kira Global Witness mai hedkwata a London ta fitar a rahotonta.
Kungiyar ta Global Witness, ta bayyana cewa kamfanin kasar wajen, ya biya manyan jami’an gwamnati sama da dala dubu Dari tara da hamsin, domin mallakar wani filin hakar ma’adinai a shekarar 2010.
Rahoton ya yi zargin cewa Tyler ya karbi dala dubu saba’in da biyar a matsayin kudin tuntuba.
Sai dai Tyler na zargi shugaba Ellen Johson Sirleaf da hanu a kokarin da ake yi ganin an tsige shi daga mukaminsa.