A yau Litinin Kerry ya gana da shugaban Kenya, Uhuru Kenyatta, gabanin ya hadu da ministocin harkokin wajen, domin ganin an dakile sake fanjamar Sudan Ta Kudu cikin wani sabon yakin basasa. Sudan ta Kudu dai ita ce ‘yar autar kasashen duniya.
Har ila yau Kerry da sauran ministocin harkokin wajen kasashen Afrika, za su tattauna kan rikicin Somalia, wacce ke shirin gudanar da zabukan ‘yan majalisu da na shugaban kasa.
Nan gaba a cikin wannan makon ne Kerry zai yada zango a Najeriya, kasar da mayakan Boko Haram suka kashe fiye da mutane dubu 20 tun daga shekarar 2009, sannan zai tsaya ma a Saudiyya, wacce ke jagorantar dakarun hadin gwiwa domin yakar ‘yan tawayen Houthi a kasar Yemen.