Mutanen kasar Angola sun gudanar da zaben sabon shugaban kasarsu na farko cikin kusan shekaru 40, kuma a yanzu sun ce dole ya kawo dai daiton tazarar dake tsakanin attajirai da talakawa.
Duka da kasancewar kasar a matsayin ta biyu dake da arzikin mai a nahiyar Afirka, Angola na ci gaba da kasancewa daga cikin kasashen da al’ummar ta ke ci gaba da zama a wahalce, kuma wadda ke dogaro akan kayan da ake shigowa da su kasar daga kasashen ketare.
Yawncin ‘yan kasar na zama cikin talauci da rashin ayyukan yi da kuma hauhawar farashin kayan masarufi.
Sabon shugaban kasar da aka zaba, Joao Laurenco, yace yana so ya rage yawan dogaro da kasar ke yi a kan arzikin man fetur.
Ya kuma yi alkawarin zai inganta harkokin noma da masana’antu da harkokin yawon bude ido, da kiwon kifi da sauran harkokin tattalin arziki.
Jam’iyyar adawa ta zargi jagabannin gwamnatinn dake mulki da cewa suna batar da dukiyar kasar ne wajen dadadawa kawunansu ne kawai.
Daya daga cikin shugabannin adawar, Manuel Fernandes, ya bayyana cewa wannan akubar talauci ba sanadiyyar faduwar farashin man fetur bane, rashin adalcin gwamnati ne ya haifar da shi.
Facebook Forum