Rundunar sojin kasar Somalia da ke samun goyon bayan dakarun Amurka, ta kashe fararen hula 10 bisa kuskure, ciki har da wasu kananan yara uku, yayin wani samame da ta kai a kusa da garin Bariire da safiyar jiya Juma’a.
Yayin wata hira da ya yi da Muryar Amurka ta wayar tarho, Janar Ahmed Jimale Irfid, ya tabbatar da mutuwar fararen hular 10 ciki har da yara kanana da kuma wasu dattawa, yayin wani samamen hadin gwiwa a wata gona da ke garin Bariire, mai tazarar kilomita 55 daga birnin Mogadishu.
Janar Irfid, ya kuma tabbatar da cewa, mutanen ba ‘yan kungiyar Al shabab ba ne, amma da farko sun dauka manoman ‘yan kungiyar ne, domin wasu daga cikinsu na dauke da makamai, inda har aka yi harbi.
Amma ya ce basu san wanda ya fara harbin ba.
Janar din ya kara da cewa a lokacin da lamarin ya faru, dakarun Amurka na wurin, amma ba shi da tabbacin ko suna daga cikin wadanda suka harbe manoman.
Facebook Forum