Kwamishinan kungiyar tarayyar turai, ya ce Brussels za ta dauki matakin katse tallafin da take baiwa kasashen da bakin haure ke fitowa daga nahiyar Afirka da Asiya, tare da saka ka’idoji kan harkokin kasuwanci, da ba da takardun visa, domin a tilasta musu karbar bakin hauren da ba su sami mafaka ba.
A wata hira da aka yi da shi a jaridar The Time ta Burtaniya a jiya Asabar, Dimitris Avramopoulos, ya ce shugabannin kungiyar ta EU, na duba yiwuwar daina ba da kudade da aiwatar da wasu manyan ayyuka a kasashen, wadanda aka kirkiro domin hana mutanen yankunan ficewa daga kasashensu.
Ya kuma kara da cewa kasashen da ba su ba da hadin kai ba, za su iya fuskantar fushin hana su takardun visa.
A kwanan nan, kasar Jamus ta yi barazanar hana jami’an kasashen da bakin hauren ke fitowa takardun visa, domin sun ki ba da hadin kai wajen karbar bakin hauren da aka mayar da su kasashensu.
A cewar Dimitris, ana duba yiwuwar saka jami’an diplomasiyya da likitoci da dalibai da masu bincike a cikin rukunin wadanda ake so a fara hanu su takardun visar, wadanda suka fito daga kasashe da ba sa karbar bakin haurensu idan aka maida su gida.
Facebook Forum