Wata kungiya mai zaman kanta da ke bin diddigin harkar manoma da makiyaya da ake kira FRAPS a takaice, ta shirya wani taron bita da ya tattaro manoma da makiyayan Jmahuriyar Nijar domin a tattaunawa.
Kungiyar ta tattaro bangarorin biyu ne daga jihohin Maradi da Damagaram da Diffa domin kara karfafa dangantakar da ke tsakaninsu ta yadda za a rika kaucewa rikici da kan taso ya haddasa hasarar rayuka da dukiyoyi.
A Jamhuriyar Nijar, rikicin manoma da makiyaya, matsala ce da aka sha fuskanta a kasar ta yadda akan shirya taruka daga bangaren gwamnati da kungiyoyi irinsu FRAPS kan kaucewa aukuwar rikici-rikicen.
Mafi yawan rikice-rikicen kan samo asali ne daga batun afkawa gwanakin manoma da makiyaya kan yi dabbobinsu, ko kuma su manoman su yi noma a kan burtalin makiyaya.
Shugaban kungiyar manoma da makiyaya na kasa, Abdu Nino Gajango ya ce maksudin wannan taro shi ne “mu hada su ta yadda za su zauna lafiya, su guji rashin zaman lafiya, su gane cewa ba abu ne mai kyau ba.”
Taron ya gudana ne a jihar Damagaram.
Saurari rahoton wakiliyar Sashen Hausa na Muryar Amurka Tamar Abari daga Damagaram domin jin karin bayani kan wannan taro:
Facebook Forum