Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Kabilar Rohingya Sun Musanta Bayanan Sojojin Myanmar


Yayin da ake taimakwa wasu 'yan kabilar Rohingya tserewa daga rikicin Myanmar a ranar 31 watan Agusan, 2017.
Yayin da ake taimakwa wasu 'yan kabilar Rohingya tserewa daga rikicin Myanmar a ranar 31 watan Agusan, 2017.

'Yan kabilar Rohingya sun musanta zargin da sojojin kasar suka yi na cewa sun kashe Musulmi masu ta da kayar baya inda suka ce su aka kai wa hari aka kashe masu dumbin mutane.

Rundunar sojin kasar Myanmar, ta ce akalla mutane 400 ne suka mutu a wani rikici da ya barke a jihar Rhakine cikin makon da ya gabata, kuma mafi yawansu Musulmi ne masu ta da kayar baya.

Shafin yanar gizon rundunar sojin kasar ta Myanmar ya nuna cewa masu ta da kayar baya 370 suka mutu, sannan ‘yan sanda da fararen hula suka kashe mutum 29.

Sai dai al’umar Musulmi ‘yan kabilar Rohingya wadanda suka kasance tsiraru a kasar, sun musanta wannan ikararin na sojojin, inda suka ce an kai musu hari a kauyukansu, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane da dama, sannan wasu dubbai sun tsere cikin jeji.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, akalla mutane 38,000 ne suka tsallaka zuwa cikin Bangladesh daga Myanmar, kuma mafi yawansu ‘yan kabilar ta Rohingya ce.

Shugabanni a kasar ta Bangladesh sun fadawa Muryar Amurka cewa akwai ‘yan kabilar Hindu wadanda su ma tsiraru ne da suka tsallaka zuwa kasar.

Wadansu majiyoyin, sun kuma fadawa Sashen Bangla na Muryar Amurka cewa mutane da yanwasu ya kai 60,000 ne suka shiga kasar cikin kwanaki takwas din da suka gabata.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG