Koriya ta arewa ta tabbatar da cewa ta harba wani makami mai linzame wanda ya bi ta kan kasar Japan, gwamnatin kasar ta ce gwajin na maida martani ne akan atisayen hadin guywar da Koriya ta kudu da Amurka ke yi.
A safiyar yau Laraba kamfanin dillancin labaran koriya ta arewa na KCNA ya ambaci shugaba Kim Jong Un na cewa shirin harba makamin mai linzamen Hwasong 12, mai matsakaicin zango “tamkar ainihin yaki ne” kuma wannan shine mataki na farko da dakarun koriya ta arewa suka dauka akan shirin kai farmakin da suke a yanken tekun Pacific “kuma wannan muhimmin shirine na mamaye tsibirin Guam.
Shugaban kasar koriya ta kudu Moon Jae-in da na Japan Shinzo Abe sun amince ta wayar tarho yau Laraba akan cewa akwai bukatar a dauki matakan matsin lamba don a shawo kan Koriya ta arewa ta hau teburin sulhu don kawo karshen rikicin dake faruwa.
Shi kuma ministan harkokin wajen China Wang Yi, ya fadawa manema labarai yau Laraba cewa China na aiki da sauran shugabannin kasashen dake kan Kwamitin Sulhun MDD, kuma suna fata kokarin da suke yi zai taimaka wajen warware takaddamar da ake yi akan dakile shirin makaman nukiliya cikin lalama.
Facebook Forum