Duk da yake dai farashin Shinkafa yanzu a Najeriya ya ninka yadda yake a baya, inda wasu ke ganin cewa rashin noman Shinkafar da zata wadaci kasar, haka kuma an hana shigowa da Shinkafa cikin Najeriya haka yasa farashinta yayi tashin gwauran zabi. A yayin da yake karin haske kan wannan batun Mallam Garba yace a iya saninsa gwamnatin Najeriya bata hana shigowa da Shinkafa kwata kwata ba daga kasashen waje.
Gwamantin Najeriya ta haramta shigowa da shinkafa takan iyakokin Najeriya, amma bata teku ba, domin hanyar Teku itace hanya kadai da gwamnatin Najeriya ta amincewa duk wasu manoma da yan kasuwa su shigo da kayan abinci musammam ma shinkafa. Kasancewar a tashoshin jiragen ruwa dake bakin Teku nan ne ma’aikatan Kwastam da na kula da lafiya suke.
Shigowa da shinkafa ta kan iyakokin Najeriya, kamar shigowa da kayan ta kasar Nijar ko Kamaru da dai sauran makwabta na kawo matsala ga gwamnatin Najeriya, domin babu ma’aikatan da ya kamata ace sun duba kayan sun kuma karbi harajin da ya kamata gwamnatin Najeriya ta karba.
Mallam Garba Shehu dai yace maganar gwamnatin Najeriya ta haramta shigowa da Shinkafa cikin kasar ba haka yake ba, ga duk mai son shigowa da shinkafa Najeriya tabbas sai dai ya shigo da ita ta bakin teku kamar yadda gwamnati ta tsara.
Domin karin bayani.