Daga zaben shekarar dubu biyu da goma sha daya wato 2011 'yan siyasa suka kuts kansu cikin dandalin.
Sun yi anfani da bayyana manufofinsu amma daga baya kuma ya koma na yada kiyayya tare da bayyana karerayi.
Kwana kwanan nan aka bada labarin sacewar babban sakataren majalisar muslunci ta duniya al-Turki a babban masallacin Abuja. Jaridar The Nation ce ta fara buga labarin. Amma kafar labaran yanar gizo ta canza abun da alakantashi da tada fitinar muhawarar kungiyoyin Boko Haram da sufaye a Najeriya. Amma daga bisani Sheikh Yakubu Hassan Katsina ya musanta batun.
A makon da ya gabata ma ne 'yan Facebook din suka bada labarin karya cewa Allah ya yiwa Shaikh Sani Yahaya Jingir rasuwa amma nan take Sagir Sambo Rigachukun ya yi watsi da labarin. Ya gargadi musulmi su daina yada jita-jita musamman akan mutanen da shugabanci ya rataya a kansu domin zasu tsoratar da al'ummar musulmi akan abun da bai dace ba.
Suleiman Hashim wanda ya yi tattaki daga Legas zuwa Abuja domin nuna murna lashe zaben da shugaba Buhari ya yi shi ma ya shiga tarkon masu yada jita-jita ta yanar gizo. An ce wai ya yi nadamar goyon bayan Buhari kuma ya yi niyar tashi daga Abuja zuwa Legas domin nuna adawa da abun da yake ganin Buharin ya gaza.
Suleiman Hashim ya yi tattaki zuwa ofishin Muryar Amurka dake Abuja domin karyata jita-jitar. Yace duk abun da aka fada kanshi dangane da shugaba Buhari babu kanshin kaskiya ciki. Yace har gobe suna tare da Buhari.
To saidai tsohon minista injiniya Mustapha Bello yace jita-jitan na tasowa ne saboda rashin bada labarai da jami'an gwamnati ke yi. Wadanda ya kamata su bada labari daga bangaren gwamnati suna yin shiru lamarin da kan sa mutane suna kame-kamen labari.
Ga karin bayani