Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Democrats Suna Nemi Bayanai A Kan Guguwar Da Ta Abkwa Kasar A Bara


Shugabat Donald Trump
Shugabat Donald Trump

‘Yan jam’iyar Democrat a majalisar dokokin Amurka sun ce zasu sake komawa bincike kan matakin da gwamnatin Trump ta da dauka bayan guguwar Maria.

A watan Satumba shekara ta dubu biyu da goma sha bakwai wata guguwa da matsanancin ruwan sama suka keta tsibitin Virgin Island da Puerto Rico, ta kashe kimanin mutane dubu uku a Puerto Rico ta kuma yi barnar gaske.

Har yanzu wadansu sassan yankin na Amurka basu da muhimman ababan jin dadin rayuwa da suka hada da ruwan famfo da wutar lantarki.

Kwamitin sa ido kan ayyukan gwamnati da dan jam’iyar Democrat Elija Cummings ke jagoranta, ya aikawa fadar White House da wasika jiya Litinin da ma’aikatar lafiya da kuma hukumar agajin gaggawa yana bukatar bayanan matakan da gwamnati ta dauka bayan aukuwar guguwar.

Masu kushewa lamura sun ce matakan da shugaba Donald Trump ya dauka bayan guguwar basu dace ba, da kuma cewa da ya yi gwamnatin Puerto Rico bata da godiya.

Ya bayyana a wani sakon twitter da ya dora a shafinsa cewa, majalisa ta ba Puerto Rico dala miliyan dubu casa’in da daya na tallafi. Yace ‘yan jam’iyar Democrat suna barazanar kin amincewa da kudurin da zai bada izinin taimakawa jihohin tsakiyar yammacin kasar da suka fuskanci ambaliyar ruwa har sai an kara ba Puerto Rico wani tallafin kudi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG