Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Na Niyar Sauke Shugaban Venezuela Da Karfi Tuwo


Donald Trump da Mike Pompeo sakataren harkokin wajen Amurka
Donald Trump da Mike Pompeo sakataren harkokin wajen Amurka

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo yace Amurka ta kimtsa ta kai gudunmuwar soja domin dakile rashin kwanciyar hankali dake faruwa a Venezuela.

Akwai yiwuwar gudanar da ayyukan soji, inji babban jami’in diflomasiyar Amurka yana fada a shirin Fox Business Network. Indai yin hakan zai kawo matsalaha, toh abin da Amurka zata yi kenan.

A halin da ake ciki, Pompeo ya nanata cewa Amurka ta fi so a sauya mulki cikin lumana a Caracas daga shugaba Nicholas Maduro dan gurguzu zuwa ga Juan Guaido wanda ya ayyana kansa shugaban kasa na wucin gadi na majalisar dokoki, wanda Amurka da wasu kasashe hamsin suka amince da shi a matsayin shugaban kasar ta nahiyar kudnacin Amurka.

Pompeo ya bayyana alamu cewa Amurka ka iya aika sojoji a Venezuela domin gaggauta mai da martani ga ayyukan Rasha, babbar mai marawa Maduro baya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG