Daraktan yada labarai na rundunar Kanal Sani Usman Kukasheka ya bayyana sabon salon yakin da suke anfani dashi.
Yace barin wuta da ake yi masu daga sama har kasa ya tarwatsasu. Kuma an bi duk wata hanya da suke samun abubuwan masarufi an toshe saboda haka abun ya zame masu alakakai.
Galibinsu sun fara mika wuya. Wadanda suka fito suna bada labarin cewa yasu-yasu lamarin bashi da dadi. Kowa na neman ta yi ta kansa.
Kawo yanzu 'yan Boko Haram da dama daga bagarorin Gwozah da Bama da wasu wurare suke fitowa kuma ana kan lissafi tare da tantancewa.
Babban abun dake jan hankalin masana tsaro shi ne yadda manyan hafsoshin sojin kasar suka tare a jihar Borno ba ma a birnin Maiduguri ba amma a filin daga.
Rahotanni sun nuna cewa babban hafsan sojin saman Najeriya Air Marshall Sadiq Abubakar da kansa yake jagorantar farmaki daga sama yayinda takwaransa na sojin kasa Janar Tukur Buratai na can a filin daga.
Jibrin Baba Ndace wani dan jarida mai zaman kansa dake cikin tawagar babban hafsan sojin Najeriya ya ce tafiyar da suka yi ta shirin yaki ce. Janarorin kowa na dauke da bindiga. Da sojoji suka ga kwamandojinsu cikin shirin yaki sun samu karfin gwiwar cewa su zasu je su gama dasu.
Wani kwararre kan sha'anin tsaro da yaki da ta'adanci Dr.Muhammad Dangel na Jami'ar Maiduguri ya jawo hankalin sojojin Najeriya cewa bincikensu na masana ya nuna 'yan Boko Haram sun rabu kashi hudu. Akwai masu tsatsstauran ra'ayi babu yadda za'a yi dasu su fito. Akwai wadanda sun samu kansu ciki ne basu da mafita.Akwai wadanda aka zuga suka shiga. Akwai kuma wadanda basu sani ba hankalinsu kuma bai san inda suke tafiya ba.Wadanda suke cikin na farko ya kamata a yi masu hukunci da wuri.
Ga rahoton Hassan Maida Kaina.