A kan batun tsaro Sanata Ndime yace jama'a da duniya suna gani akwai cigaba da aka samu.
Yanzu akwai hadin kai na kasashe wanda a da babu shi. A manyan kasashen duniya da aka dangana dasu su bada tallafi yanzu sun farga daga zuwan shugaba Buhari. Duniya ta samu karfin gwiwa na niyar taimakawa.
Ana samun nasara. Misali muanen Gwozah sun fara matsawa suna son su koma gidajensu da suka baro. Yanazu ana tanadin yadda za'a mayar dasu.
Kamar yadda shugaban kasa ya fada kafin karshen wannan shekarar za'a gama da kungiyar Boko Haram.
Makon jiya sama da mutane dubu sun bar Maiduguri sun koma yankunansu. Gwamnan jihar Borno ya taimaka da motoci kana sojoji suka yi masu rakiya.
A Gwozah an fara cin kasuwa. Masllatai na gudanar da sallar Juma'a haka kuma mijami'u na sujada ranar Lahadi.
Dangane da hare-haren da har yanzu 'yan kungiyar suna kaiwa Sanata Ndime yace ba zasu dauke rana daya ba. Yanzu babu tashin bam kamar da.Yanzu ma harin da suke yi na neman abinci ne.
Yanzu 'yan Boko Haram basu da bindigogi irin na zamani. Da adaka suke kai hari saboda duk hanyoyin samun makamai an toshe. Hanyoyin samun kudi da zasu sayi makamai babu kuma. Basu da motoci ko man fetur dalili ke nan yanzu suna kai hari kan dawaki.
Ko shakka babu karfin kungiyar Boko Haram ya ragu sosai. A kan 'yan matan Chibok kuma Sanata Ndime yace yanzu da shugabancin Buhari suna da karfin gwiwar zasu dawo.
Ga rahoton Haruna Dauda Biu.