WASHINGTON DC, —
Yayin da kungiyar boko haram suka dauki sabon salon kai hari akan dabbobi musammam dawakai suke kakkashe mutanen da ba suji ba basu gani ba, masu shharhi akan al’ammuran yau da kullun sun fara tofa albarkacin bakin su game da wannan lamari.
Jibrin Babace dan jarida ne dake kwararre a labaran tsaro, domin ko kwanan ya ziyarci sansanin da ake fafatawan tsakanin sojoji da yan kungiyar ta boko haram a jihar Borno, ga kuma abinda yake cewa game da wannan sabon tsarin kai hare-haren na yan kungiyar ta Boko Haram.
‘’To kamar abinda Hausawa ke cewa ne idan kida ya canza to rawa ma dole ya sake, sabo da yanzu kaga wuta ake bude musu daga sama da kasa ta ko ina babu sauki gare su’’
To sai dai wakilin sashen Hausa na Muryar AmurkaHassan Maina Kaina ya tambayi mai Magana da yawun rundunar sojan ta Najeriya shin ko suna sane da wannan sabon salon na yan boko haram dake kai hare-hare kan dawakai?shima ga abinda yake cewa.
‘’Mun samu labari kwarai da gaske cewa suna kai hare-hare ta anfani da dawaki, kuma yanzu haka muna iya bakin kokarin mu domi ganin mun ciwo karfin wannan al’amarin insha ALLAHU, ai shure-shure bai hana mutuwa yanzu sunga karfin ya kare abinda suke yi shine kaiwa mutane hare-hare da dawakai da sauran su.Amma abinda muke jawo hankalin mutane shine su kwantad da hankalin su.Rundunan soja suna kokari cewa an kusa kawo karshen aukuwar wannan al’amari, sai su kuma mutanen na kauyuka su taimaka muna da ainihin bayanai game da irin wadannan mutanen’’
A daya bangaren kuma rundunar sojan ta Najeriya bayan wani dogon nazari data yi na sojojin su 500 da aka yanke wa hukunci daban-daba kuma aka sallame su daga aiki, yanzu haka dai ta wanke 3,032, sai dai kuma ina matsayin sojan nan da aka yanke wa hukuncin kissa?
Ga dai abinda kakakin rundunar sojan Kanar UsmanKuka Sheka ke cewa.
‘’Abinda nake so ka gane akwai wasu hukunce-hukunce da suka jibanci wasu laifuffuka da a yi ambatan su ba, kana akwai wasu sharioi wadanda har yanzu ana ci gaba dasu saboda haka wannan sharaoi basa cikin wadanda akayi nazarin su, wani abu ne da za aci gaba dashi’’
Suma Lauyoyi dake kare hakkin bil adama a Najeriya sunyi maraba da wannan mataki kamar yadda Bar Yakubu Bawa ke cewa.
‘’Mu kammu munji dadi kwarai na yanke hukuncin da aka yanke na cewa a dawo dasu abinda akayi yayi kyau’’