Rahoton yace matakin da ka iya kawo karshen ta'adanci a kasar da aka kwashi kusan shekaru biyar ana fama shi ne mahinmmin dalilin da yasa suka amince da karbo bashin domin a sayo sabbin kayan yaki.
Sai dai Kabiru Ibrahim Gaya ya diga ayar tambaya akan batun. Yace kasar tana da kudin ba sai ta ciwo bashi ba. Idan an tuna tsohon gwamnan babban bankin kasar ya taba maganar batar dalar Amurka biliyan ashirin. Aka ce basu bata ba. Daga baya aka ce dala biliyan biyar sun bace. Majalisar dattawa tayi bincike ta gano dala biliyan daya wadda tace lallai ma'aikatar man fetur ta tabbata ta dawo da kudin.
Wata shida ke nan da yin maganar. Ministan man fetur ta kawo kudin sabili da haka me yasa kasar zata fita waje tana neman bashi. Kudin akwaisu ba wai babu ba.
Karin Bayani akan Rahoto na Musamman a Kan Boko Haram: Jini, Hawaye da Fargaba a Daular El-Kanemi >>
Sanata Gaya yace yayi iyakacin kokarinsa yayi magana a majalisa aka hanashi. Shugaban majalisa ya ki daga baya yace a yi kuri'ar baka ko an yadda ko ba'a yadda ba. Haka din ko aka yi aka ce an amince.
Wani batun da yake damun 'yan asalin jihar Borno da abun ya shafa shi ne rashin kulawa da sojoji dake bakin daga da 'yan Boko Haram da ma wadanda suka rasa muhallansu kamar yadda Sanata Ahmed Zanna ya bayyana.
Yace abun kunya ne ace za'a sayi makamai. Wadanda aka saya da gaba daya suna hannun 'yan Boko Haram. Nan gaba ma wa ya sani ko zasu sake fadawa hannunsu su yaki kasar da su. Sabili da haka Sanata Zanna yace bai ga abun da zai sa a dauko bashi wai domin sayen makamai ba.
Amma Sanata Maina Ma'aji Lawal yace amincewa da karbar bashin ya zama wajibi. Suna son sojoji a basu duk kayan da suka kamata da goyon bayan da suke so. A basu duk horon da ya kamata. Kana shugaban kasa yayi jagora su kuma su bishi domin a samu masalahar abun, wato a sake kwato wuraren da 'yan ta'ada suka kwace da kuma kai taimako ga wadanda suke cikin wahala sanadiyar tashin tashinar. Lokacin zargi ya wuce. Yanzu lokaci ne na hada kan kowa da kowa domin a cimma nasara.
Ga rahoton Medina Dauda.