Kungiyar ta zargi majalisar dokokin jihar da daurewa cin hanci da rashawa gindi a cikin jihar.
Kungiyar ta rubuta wata wasika zuwa hukumar ta EFCC inda take zargin majalisar dokokin jihar da yin kafar angulu a kokarin neman hukumta tsoffin ma'aikatan fanshon jihar da aka samesu da laifin sace sama da N261m na ma'aikatar.
Malam Muhammad Abubakar shugaban kungiyar ya bayyana dalilin da ya sa suka rubuta wasikar. Yace sun rubuta wasikar tare da aikawa gwamnan jihar daya da sakataren gwamnati daya da kuma shugaban ma'aikatar fanshon saboda wai, sun ji Majalisar Dokokin jihar ta daurewa wadanda suka yi aika aika-aikar gindi. Kungiyar ta sha alwashin dole a yi abun da ya kamata.
Sun fada a wasikarsu cewa Majalisar Jihar tana daurewa cin hanci da rashawa gindi.
A makon jiya ne Majalisar Dokokin Jihar ta kada kuri'an yanke kauna da shugaban hukumar kula da harkokin ma'aikatan jihar Alhaji Shehu Galadima saboda ya ki y aikawa majalisar rahoton da ya samu tsoffin ma'aikatan fanshon da laifin yin rub da ciki da kudi har nera milian dari biyu da sittin da daya.
Onarebul Malik Madaki Boso shugaban kwamitin kula da harkokin ma'aikata na majalisar yace suna da cikakken bayani da zasu bayar idan EFCC ta waiwayesu akan maganar.
Shi kuwa Alhaji Shehu Galadima shugaban hukumar ma'aikatan jihar ya bayyana dalilinsa na hana majalisar kwafin rahoton. Yace a matsayinsu na hukumar dauka da ladabtar da ma'aikata suna da iko su hana ba kowa rahoton abun da su keyi har sai sun gama. Yace har yanzu suna kan binciken inda kudaden suke domin su biya masu shi.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani.