Abdi Hassan Hussein, Tsohon Daraktan Hukumar Leken Asirin Tsaro ta PIA mai alaka da Amurka, ya ce lokacin da aka fafa bangaren 'yan bindigar Somaliya mai ra'ayin ISIS a watan Oktoban bara, mutane 20-30 ne kawai ciki, to amma tuni bangaren ya kafa sansanonin horo da na daukar sabbin mayaka. Ya ce yanzu mayakan kungiyar sun kai tsakanin 100 zuwa 150. "Tuni su ka yaye rukunonin farko na sabbin dauka, kuma har an ba su kayan yaki," a cewarsa.
Hussien ya shugabancin PIA har zuwa bara, lokacin da aka maye gurbinsa. Babbban aikinsa shi ne bankado shirin kai harin ta'addanci da kuma tsara yadda za a tsai da shi.
Ya ce ISIS ta yi lale-marhaban da reshenta na Somaliyan, kuma tuni ta shiga samar masa da kayan yaki, ta hannun reshsenta da ke Yemen.
Hussein ya yi nuni da wani faifan bidiyo na kwanan nan da ke nuna yadda kungiyar ke karbar inifom. Ya ce akwai kuma hujjojin da ke nuna cewa kungiyar ta amshi tallafin kudi daga ISIS.