Mashigin tekun Guinea ya zama bangaren teku da yafi kowanne hadari a duniya, inda ‘yan fashin teku suka kai hare hare hamsin da hudu bara, suka kuma yi sanadin asarar dala miliyan dari bakwai, bisa ga rahoton da kungiyar yaki da fashin teku ta Amurka da ake kira "Oceans Beyond Piracy" ta buga.
“A lokutan baya, daya daga cikin manyan hanyoyin da ‘yan fashin teku ke amfani da ita, shine fashin jiragen ruwa domin suyi sata a cikinsu” inji Mathew Walje, jagoran wallafa rahoton.
Sai dai da mayakan ruwa suka fara kai dauki da zarar an kai hare haren, ‘yan fashin tekun basu iya daukar kwanaki suna kwasar ganima a jiragen da suka yi fashi.
"Ya zama dole suka sake wata sabuwar dabarar hari da sace mutane domin neman fansa wadda bata bukatar lokaci mai tsawo,” Inji Walje.
Sufurin jiragen ruwa na taka muhimmiyar rawa a tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika kamar Najeriya da Ghana da kuma Ivory Coast, dake sufurin kayan da suke sayarwa a kasashen ketare kamar mai, da koko ta ruwa.