A wannan makon ne Kungiyar Kasashen tarayyar Afrika zata gudanarda taron farko na kasa-da-kasa kan shirin dasa itattuwa a birnin dakar na kasar Senegal. Babban burin wannan shirin dai shine fito matakan kawas da kwararowar hamada a yankin kasashen da ke yamma da hamada, abinda kwararru suka ce yana kawo talauci da rashin tsaro.
A babban taron kolin sauyin yanayi na kasashen duniya da aka yi a birnin Paris a watan Disambar bara, shugabannin kasashe sun dauki alkawarin bada taimakon dala biliyan 4 nan da shekaru 5 don farfado da yankin na Afrika. A kan haka ne yanzu wakilai daga kasashe 20 daga yankunan arewa da yammacin sahara suke ganawa da kwararru da kungiyoyi a Dakar don tattanawa akan yadda za a fitowa lamarin.
Tun shekarar 2005 aka fidda shawarar shirin da ake kira da turanci "Great Green Wall", wanda kuma tsohon shugaban kasar Senegal Abdoulaye Wade ya bada jagorancin karfafa shi.
Kudirin shine a dasa dubban itatuwa masu yawa da zai shafi yanki mai nisan dubban kilometoci daga Senegal zuwa Djibouti don magance kwararar hamada daga yankunan dake kudu da hamada.