Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yamal: MDD Ta Jibge Sojojin Houti a Wasu Muhimman Hanyoyi


Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta fada jiya Lahadi cewa sake jibge rundunar sojin Houti a wasu muhimman hanyoyin shiga Yamal ya yi daidai da tsarin da aka tabbatar.

Dakarun zaman lafiya na MDD ne suke kula da hanyoyi ukun shiga kasar a lokaci guda, ya yin da sojoji suka bar hanyoyin shiga kasar kana rundunar tsaron gabar teku suka maida hankali wurin tsaron kasar, inji Michael Lollesgaard, shugaban kwamitin MDD a kan ayyukan daukar jami’an tsaro a cikin wata sanarwa.

Sanarawar ta ce ana sa ran a ‘yan kwanaki masu zuwa za a maida hankali a kan janye sojoji da zasu sake halayensu ko kuma suka rasa kimarsu.

MDD ta shirya ta kula da aikin farko na dauke sojojin Houti, a matsayin babban matakin kawo karshen yakin da aka kwashe shekaru hudu ana yi a Yamal a ranar Talata. Aikin sake jibge sojojin Houti ya fara ne a ranar Asabar, bisa kan yarjejeniyar da aka kulla a cikin watan Disamba a kasar Sweden tsakanin gwamnatin Yamal da ‘yan tawayen Houti masu samun goyon bayan Iran.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG