Wani harin bam na kunar bakin wake da aka kai da safiyar yau dinnan Laraba a harabar wani masallaci a birni na biyu mafi girma a kasar Pakistan, wato Lahore, ya hallaka mutane a kalla 8, ya kuma raunata wasu 20.
Ana kyautata zaton wata motar 'yansanda aka auna wa harin, daura da daya daga cikin kokfofin masallacin. Jami'an 'yansanda akalla biyar ne su ka mutu a wannan harin, a cewar Arif Nawaz, babban jami'in 'yansanda na lardin Punjab.
Masallacin da Sufaye, wanda aka gina shi tun a karni na 11, wanda aka fi sani da sunan Data Darbar, na daya daga cikin mafiya girma da aka kuma fi ziyarta a kasar. An taba kai masa hari a baya, ciki har da wani harin bama-bamai a shekarar 2010, wanda ya kashe mutane 40. Tun a lokacin ya kasance cikin kulawar 'yan sanda.
Facebook Forum