Wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na GNN ta fitar, ta ce wata mota da ke dauke da kayayyaki ta bi abka kan nakiyar da aka binne da sanyin safiyar Lahadi, kimanin kilomita 6 daga kauyen Samira.
Kauyen da ke kusa da iyakar Nijar da Burkina Faso a kudu maso yammacin kasar, wanda tun a shekara ta 2004 ya zamanto wurin hakar zinare daya tilo da kasar ta samu.
Mayakan ‘yan ta’adda suna kai hare-hare a kai a kai a yankin.
Wannan harin dai shi ne na baya bayan nan a jerin hare-haren da aka kai wa sojojin Nijar.
Kasar ta yankin Sahel mai fama da talauci na fama da tashe tashen hankula daga yan ta’adda masu alaka da al-Qaida da kungiyar IS. Haka kuma a yankin Kudu maso Yamma ta na famar artabu da mayakan Boko Haram.
Kasashen yammacin duniya da dama ne ke taimaka mata, ciki har da Faransa da Amurka, wadanda dukkansu ke da sansanonin soji a can.