Rahotanni daga garin Gudunbali da ke jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya na cewa, al’amura sun lafa, bayan wani hari da mayakan boko Haram suka kai a garin.
Wata sanarwa dauke da sa hannun kakakin rundunar sojin Najeriya, Brig. Gen. Texas Chuckwu, ta bayyana cewa dakarun Najeriya sun sake hadewa wuri guda, bayana wata arangama da suka yi da mayakan Boko Haram, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
A cewar sanarwar, dakarun na Najeriya sun fatattaki maharan daga garin bayan wani artabu da suka yi da su.
Da maraicin ranar Juma’ar da ta gabata, mayakan na Boko Haram suka far ma garin na Gudunbali da manyan makamai a cikin motoci.
Mataimakin gwamnan jihar Borno, Alhaji Usman Durkwa ya tabbatawa da Muryar Amurka aukuwar wannan lamari.
Wannan hari ya sa jama’ar gari na Gudunbali suka fice domin tsira da rayukansu.
Sai dai bayanai sun ce mayakan kungiyar ba su taba farar hula ba.
“Ranar Juma’a da maraice da misalin karfe 5 suka zo, suka kwana sai kamar da karfe 4 na asuba suka fice.” Inji wani da ya arce daga garin na Gudunbali da ke karamar hukumar Guzamala.
Babu rahotanni da ke nuna cewa an samu asarar rayuka, amma maharan sun kona wasu wuraren da sojoji ke zama.
“Ba su taba kowa ba, sun ce babu ruwansu da kowa,” sai dai sun yi ta neman jami’an tsaro, a cewar mutumin da ya yi magana da Muryar Amurka, wanda ya nemi a boye sunansa.
A watan Mayun wannan shekara aka bude garin na Gudunbali tun bayan da al’umarsa ta fice sanadiyar hare-haren da ya fuskanta a baya.
Saurari cikakken rahoton wakilin Muryar Amurka, Haruna Dauda Biu.
Facebook Forum