Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu 'Yan Gudun Hijira Sun Samu Taimako A Taraba


Kayan tallafi da aka taimakawa 'yan gudun hijira a Taraba
Kayan tallafi da aka taimakawa 'yan gudun hijira a Taraba

Daruruwan yan gudun hijiran da tashe tashen hankula ya raba da gidajensu a jihar Taraba sun koka game da halin da suke ciki inda suke zargin cewa gwamnatin jihar ba ta kulawa da su,zargin da hukumomi ke musantawa duk da cewa wasu kungiyoyi na taimaka masu.

Su dai wadannan yan gudun hijira da tashe tashen hankula ya raba su da gidajensu yanzu haka sun shafe makwanni a Jalingo a sansanonin wucin gadi,inda suke kokawa game da halin da suke ciki,musamman ta fuskacin cimaka,ga kuma zargin da suke yi na cewa an maida su saniyar ware.

Yan gudun hijiran dai sun ce in baicin taimako da suka samu daga wasu kungiyoyin sakai na kasa da kasa ba wani tallafi da suka samu daga bangaren gwamnatin jihar Taraban.

Yayinda suke yabawa kunyiyoyin kasa da kasa da ke kawo masu tallafi, sun kira gwamnati ta taimaka masu. Wata ta ce ta samu shinkafa da bokiti da dai sauran kayan da za su taimaketa.

Mr James Gwani shine mataimakin shugaban 'yan gudun hijira da ke anguwan Abuja Phase II,ya bayyana halin da suma suke ciki. A cewarsa gwamnatin jihar ba ta dauki wani matakin taimaka masu ba sai dai kungiyoyin da ke tabukawa

Shugabar kungiyar dakile kissan gilla a jihar Taraba Hajiya Aisha Bashir Ardo na cikin masu taimakawa 'yan gudun hijiran a yanzu, ta bayyana kokarin da suke yi. Ta kira a taimakawa wadanda suka bar gidajensu domin su sake gina muhallansu. Ta ce kawo yanzu suna da 'yan gudun hijira sama da dubu 18. Idan an taimaka masu da kayan gini wasu za su iya komawa su ci gaba da rayuwarsu. Daga karshe ta kira hadin kai tsakanin gwamnati da kungiyoyin dake kawo taimako.

To ko me hukumomin jihar Taraban ke cewa ne game da zargin shakulatin bangaro da yan gudun hijiran ke yi a yanzu? Mr Nuvalga Danagbo shine shugaban hukumar kai dauki ta jihar ,SEMA, ya bayyana kokarin da su keyi. Ya ce ba su yi watsi da su ba domin suna kai masu abinci tare da lura da lafiyarsu. Amma yanzu suna jiran gwamnati ta ba su kudi su sake ma 'yan gudun hijiran matsuguni.

A saurari rahoton Ibrahim Abdilaziz domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:22 0:00

A saurari rahoton Ibrahim Abdulaziz

Facebook Forum

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG