Sai dai kuma kungiyar kwadagon jihar Borno, ta ce bata gamsu ba da yadda ake biyan kudaden, duk da cewa yabawa gwamnnan jihar game da sakin kudaden da ta yi. Amma idan aka duba kudin cikin Naira Biliyan 20 da ake bin gwamnati kashi 10 cikin 100 kadai ta iya biya.
Shugaban ma’aikatan jihar Borno, Yarima Sale, ya sanarwa da manema labarai ya ce tuni an fara biyan mutanen da suka kammala wa’adin aikinsu a jihar.
Kungiyar kwadagon dai ta koka kan cewa kudaden sunyi kadan matuka, idan aka kwatanta da yawan basussukan wadanda suka yi ritaya ke bin gwamnatin.
Kwamarad Titus Ali, shine shugaban kungiyar kwadagon jihar Borno, ya ce “Idan aka duba yawan kudaden da jihar Borno ta saki, duk da cewa mun yaba da abin da suka yi, amma ba abin azo a gani bane, domin ba zasu yi wani tasiri ba ga mutanen, saboda yawansu da yawan kudaden da suka taru.”
Ya ci gaba da cewa idan ba don gwamnati ta amince da fara biyan kudaden ba, dukkan ‘yan kungiyar kwadago zasu dunguma cikin yajin aiki, amma yanzu dai an daga mata kafa.
Kudaden sun taru ne saboda dakatar da biyan Naira Miliyan 150 da gwamnatin jihar Borno ke yi duk wata, ga mutanen. Kuma kungiyar kwadago ta yi fatan cewa gwamnati za ta ci gaba da biyan kudaden, domin taimakawa mutanen da suka bautawa jiha har na tsawon shekaru 35.
Domin karin bayani saurari rahotan Haruna Dauda.
Facebook Forum