A Jamhuriyar Nijar an gudanar da wani kwarya-kwaryar bikin kona daruruwan ton-ton na magunguna hade da tarin wasu ababen sanya maye.
Wannan wani yunkuri ne da ke hangen kariya daga illolin irin wadannan magunguna da suka mamaye kasuwannin kasar ba a kan ka’aida ba.
Magungunan wadanda yawansu ya kai ton 915, wasu daga cikinsu an shigo da su ne daga waje ta barauniyar hanya wato ba da izinin ma’aikatar kiwon lafiya ba, yayin da wasu kuma magunguna ne na jabu, sai rukuni na 3 da aka gano cewa ana sayar da su a kasuwanni a wani lokacin da wa’adin amfani da su ya riga ya wuce.
Watanni akalla 9 aka shafe ana farautar irin wadannan magunguna da ke barazana ga lafiyar jama’a, kamar yadda shugaban ofishin hukumar Douane ko kuma Kwaston na jihohin Tilabery da Yamai, Kanal Ali Hamani ya bayyana, ya na mai tabbatar da cewa sun bi hanyoyin da ya kamata a shari’ance kafin gudanar da aikin kona wadanan magunguna.
A wani bangare na wannan kwarya-kwaryan biki, hukumomi sun kona kayayyakin zukar tabar Shisha kimanin 51,000 wadanda ‘yan sanda suka cafke a unguwannin birnin Yamai bayan da gwamnan jihar ya kafa dokar hana shan Shisha a ranar 24 ga watan Yulin 2024.
Matakin da aka ayyana a matsayi na kare matasa daga barazanar da wannan mummunar dabi’a ke yi wa lafiyar kwakwalwa.
Kwamishiniyar ‘yan sanda Zouera Haoussaize ita ce shugabar Sashen kula da kare yara da mata a hukumar ‘yan sanda ta kasa, ta ce Shisha tana hallaka yara gaskiya, kuma yaran suna shiga wani hali wanda ba shi da dadi.
Gwamnan Yamai Janar Assoumane Harouna, wanda ya jagoranci bikin ya jinjina wa ma’aikatan.
A cewarsa, za su ci gaba da karfafa matakan yaki da irin wadannan kayayakin da ke cutar da al’umma da salwantar da makomar matasa.
Magungunan jabu da wadanda ake shigo da su ba akan ka’ida ba, wata hanya ce ta samar da makudan kudade ga wadanda suka rungumi wannan haramtacciyar sana’a, dalili ke nan ake kara samun yawaitar kasuwannin sayar da su a kasashe masu tasowa duk da matakan da hukumomi ke dauka, da alama talauci da jahilcin jama’a na kara wa abin armashi.
Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma:
Dandalin Mu Tattauna