Dubun wadannan masu fataucin magungunan jabu ta cika ne yayinda jami’an tsaro suka riske su a lokacin da suke kokarin sauke lodin kwalayen magunguna domin jibge su a wani dakin ajiya dake birnin Niamey, lamarin da ya ba hukumar yaki da mugayen kwayoyi damar zurfafa bincike da a karshe aka kama kwalaye dubu daya da dari takwas da goma sha uku, dukansu shake da magungunan jabu.
Kyaftin Nana A’ishatu Usman Bako, ita ce kakakin ‘yan sandan jamhuriyar Nijer, ta bayyana cewa wani matum dake da lasisin shigar da magunguna kasar ne ya taimaka wajan shigar da magungunnan jabun.
Babban alkali mai shigar da kara da sunan gwamnati Chaibou Samna, ya ziyarci ofishin hukumar domin ganewa idon sa wadannan kwalaye, kuma ya yaba da wannan kokari da hukumar ta yi, ya kuma bada tabbacin hukunta dukkan wadanda suke da hannu a wannan haramtacciyar sana’a.
Da aka gabatarwa da ‘yan jarida magungunan wadnda suka hada da Dicloxacline 50mg, da Co-trimoxazole 480 da sauransu, sun sun banbanta da na ainihi. Masana sun bayyana cewa amfani da irin wadannan magunguna zai Haifar wa dan’adam illa a maimakon magance ciwo, dalili Kenan da aka yi kra ga jama’a su sa hannu wajan wannan yaki.
Wakilin muryar Amurka a yamai Sule Mumuni Barma ya aiko mana karin bayani.
Facebook Forum