Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Saki Sunday Igboho Daga Gidan Yari A Jamhuriyar Benin


Sunday Igboho
Sunday Igboho

An saki wani dan fafutukan Najeriya Sunday Adeyemo, wanda ake tsare da shi a kasar Benin tun a bara, bisa zarginsa da yunkurin tayar da kayar baya a Najeriya, a karkashin kulawar shari’a, kamar yadda daya daga cikin lauyoyinsa ya bayyana a ranar Talata.

Adeyemo wanda aka fi sani da suna Sunday Igboho, dan kabilar Yarbawa ne kuma ya yi fice tare da yin kira da a fatattake makiyaya daga kabilar Fulani daga kasashen Yarbawa a kudu maso yammacin Najeriya.

An kama shi ne a watan Yulin da ya gabata a filin jirgin saman Cotonou lokacin da yake kan hanyar zuwa Jamus, bayan da wata hukumar tsaron Najeriya ta ce ta gano tarin makamai a gidansa.

An sake shi ne a yammacin ranar Litinin din da ta gabata saboda dalilai na lafiyar jikinsa, tare da sharadin ba zai iya barin kasar Benin ba, in ji daya daga cikin lauyoyinsa da ya bukaci a sakaya sunansa har sai an gudanar da taron manema labarai.

Mukarraban sa ne kawai za a ba su damar shiga gidansa da ke Cotonou babban birnin kasuwancin Benin, wanda ‘yan sanda za su sanya ido a kai, in ji lauyan.

Kame Igboho dai ana kallonsa a matsayin wata alama ta kara zafafa kokarin gwamnatin Najeriya na bin mutanen da ake ganin barazana ce ga tsaron kasa, har da fiye da kan iyakokinta.

Hakan ya zo ne jim kadan bayan da shugaban ‘yan awaren Nnamdi Kanu, daga kabilar Igbo da ke da tushe a kudu maso gabashin Najeriya, aka dawo da shi Najeriya bisa zarginsa da ta'addanci, kashe-kashen mutane da cin amanar kasa. Kanu da lauyoyinsa sun ce an tsare shi kuma an cin zarafinsa a Kenya ba bisa ka'ida ba kafin a mika shi, lamarin da Kenya da Najeriya suka musanta.

Tun da farko dai kafafen yada labarai sun ce Najeriya na neman a mika Igboho, amma ba a san halin da wannan bukata ta ke ciki ba. Hukumomin Najeriya dai ba su amsa bukatur yin tsokaci kan lamarin Igboho ba.

- Wannan labarin kamfanin dillancin labarai na Reuters ne wanda Hadiza Kyari ta fassara.

XS
SM
MD
LG