Wata kotu a Abuja ta yankewa dan tsohon shugaban kwamitin yin garanbawul ga sha’anin fansho Abdulrasheed Maina hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekara 14.
A ranar Alhamis Alkali Okon Abang na kotun tarayya da ke birnin na Abuja a Najeriya, ya yankewa Faisal Abdulrasheed Maina hukuncin bayan da aka same shi da laifin halalta kudaden haram.
Kotun ta yanke hukuncin ne yayin da Faisal baya nan, amma ta ba da umarnin duk inda yake ya mika kansa don a kai shi gidan yari.
Alkali Abang har ila yau ya ba da umarnin cewa idan Faisal ba ya cikin Najeriya, hukumomin kasar su bi tsarin da doka ta tanada wajen maido da shi kasar.
A watan Okobar 2019, hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta gabatar da Faisal a gaban kotu, amma an ba da belinsa a watan Nuwambar 2019 akan naira miliyan 60 yayin da wanda ya tsaya masa ma ya biya wannan adadi.
Tun kuma daga lokacin aka daina jin duriyarsa a duk lokacin da kotun za ta yi zaman sauraren karar, abin da ke nufin ya tsallake beli ya gudu kenan.
Kotun har ila yau ta ba da umarnin Faisal ya mayarwa da gwamnatin tarayya kudin da yawansu ya kai naira miliyan 58.1.
Gidan talabijin na Channels ya ruwaito lauyan Fasail Anayo Adibe yana cewa hukumomin tsaro sun jima da kama Faisal a Sokoto inda ya nemi kotun ta bude bincike kan inda yake.
A watan Fabrairun bana, EFCC ta ba da rahoton cewa Faisal ya tsere zuwa kasar Amurka.