Wannan kisa dai ya auku ne a garin Patiskum dake jahar Yobe, inda saurayin ya daba wa mahaifiyar sa da kuma mahaifin sa wuka, sa’an nan ya sake kashe kannen sa guda biyu a sakamakon miyagun kwayoyi da aka ce ya sha.
Mai Magana da yawun ‘yan sandan jahar ya tabbatar wa sashen Hausa na muryar Amurka ta wayar tarho cewa yanzu haka wannan saurayi yana hannun su, kuma suna gudanar da bincike a kansa kuma ba da dadewa ba zasu gurfanar da shi gaban kuliya.
Wakilin sashen Hausa Haruna Dauda ya tuntubi dan’uwan matashin da ya aikata kisan ta wayar tarho inda ya bayyana masa cewa matashin mai shekaru 26 da haihuwa kanen sa ne kum uwar su guda uban su guda, kuma bashi da wata matsalar rashin lafiya dake da nasaba da kwakwalwa, kuma baya ga mutane hudu da ya hallaka a yayin da suke barci, yayi yunkurin buge abokin sa da cebur.
A cewar sa, bayan ya gama aikata kisan ne jama’a suka taru suka daure shi kana suka kira jami’an tsaro suka zo suka tafi da shi, ya kara da cewa su tara ne daga wurin ma’haifin nasu kuma suna zama ne a unguwar Malale dake Patiskum a jahar Yobe.
Ga rahoton Haruna Dauda Daga Maiduguri.