Hajiya Hafsat Sadeeq tace dole su bada tasu gummawar wajen taimakawa matan da suka rasa mazajensu a filin daga da kuma samarin dake tasowa domin koyas dasu sana'o'i daban daban su ma su zamo masu dogaro ga kai nan gaba.
Hajiya Hafsat ta bayyana hakan ne lokacin da ta kaddamar da wani shirin taimakawa mata da matasa dari da hamsin a makarantar Ramat dake birnin Maiduguri.
Yanzu sun zabo matan da suka rasa mazajensu a filin daga da wasu dalibai da suka hada da samari da 'yan mata da za'a koyas dasu sana'o'i iri-iri har da karatun kwamfuta nan da sati shida.
Mutanen da aka dauki nauyinsu sun bayyana jin dadinsu. Sun yi godiya tare da yi mata addu'a. Suna fatan zasu samu sana'o'in da zasu dinga yi yayinda suke cigaba da karatunsu.
Ga karin bayani.