Wata uwa mai matsaikatan shekaru da ‘ya’yanta 2 sun kone a wata mummunar gobarar data afku a birnin Ondo, shelkwatar karamar hukumar Ondo ta Yamma ta jihar.
Rahotanni sun ce al’amarin ya faru ne a daren Lahadin data gabata a gidan mamatan dake kan titin Rainbow daidai mahadar lipakala dake daura da titin Adeyemi, a tsohon birnin.
A cewar wata majiyar iyalan, wacce ta nemi a sakaya sunanta, mutanen sun kone kurmus har ba’a iya ganesu.
Majiyar ta kara da cewar gobarar wacce ta shafe sa’o’i tana ci ta lalata ilahirin ginin.
Da take tabbatar da afkuwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ondo, CSP Funmilayo Odunlami, wacce ta bayyana lamarin da abin takaici, tace an adana gawawwakin wadanda suka mutun a dakin adana gawa na wani asibitin dake birnin.
Dandalin Mu Tattauna